Kungiyar tsofaffin daliban Rumfa (RUMFOBA) Class ’94 ta yi bikin cika shekaru 30 a Kano, inda ta bukaci kafa cibiyoyin adana bayanai a kowace unguwa domin inganta tsare-tsare da ci gaba.
Shugaban kungiyar, Farfesa Ibrahim Sani Madugu, ya jaddada mahimmancin cibiyoyin wajen tsaro da bunkasa tattalin arziki.
Kungiyar ta gudanar da ayyuka a makarantar su, ciki har da samar da ruwa, sanya CCTV, da fitilu masu amfani da hasken rana.
A taron, an karrama mutane uku ciki har da Malam Ibrahim Shekarau da Dr. Yusuf Ibrahim Kofar-mata saboda gudunmawarsu ga ilimi.
Dr. Kofar-mata ya bukaci kungiyar ta mayar da hankali kan babban aiki daya a shekara.