Bincike: Yadda akayi watsi da aikin samar da lantarki mai aiki da hasken rana na Milyoyin naira a jami’ar Bayero kano

BUK 1 2
BUK 1 2

A kokarinta na samar da wutar lantarki a tarayyar Najeriya, a shekarar 2019 gwamnatin tarayya ta kaddamar da tashar samar da hasken wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Jami’ar Bayero Kano (BUK), kan biliyoyin naira da aka baiwa wani kamfanin kasar Jamus. A cikin wannan bincike, Elijah Akoji, ya bankado yadda hakan ya bar sassan jami’ar, dakunan karatu, dakunan kwanan dalibai, da ma manyan ofisoshi a hannun janareto.

Dalibai sun yi ta kokawa, malamai sun yi ta hayaniya, ma’aikatan gudanarwa a matakai sun fusata, yayin da wasu sassa da kuma dakin karatu ke amfani da injinan janareta, yanzu haka an rufe su kafin lokacin da aka saba ganin yadda samun wutar lantarki yayi karanci ga dalibai sama da Dubu 55,815 da ma’aikatan Jami’ar Bayero Kano (BUK) 3,077.

Bjnciken yw nuna an kashe makudan kudade wajan samar da megawatts 7.1 na wutar lantarki mai amfani da hasken rana wanda aka tsara don samar da wutar lantarki ga al’ummar jami’ar. “Babban almubazzaranci a ce anyi watsi da tashar samar da hasken rana mai karfin megawatts 7.1.

A shekarar 2019, Gwamnatin Tarayya karkashin shirinta na samar da ilimi mai kuzari (EEP), shirin da Hukumar Raya Wutar Lantarki a Karkara (REA) ta aiwatar, ta gina tashar samar da hasken rana mai karfin megawatts 7.1, daya daga cikin manyan ayyukan hasken rana a Afirka wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar a Jami’ar Bayero Kano (BUK).

Mataimakin shugaban kasar ya tabbatar da cewa ana kashe miliyoyin kudade a duk shekara wajen sayen man fetur da dizal domin tafiyar da wannan cibiyoyin jami’a.

Kamfanin sarrafa hasken rana wanda a cewar dalibai ya yi aiki na tsawon watanni 6 bayan kaddamar da aikin, kuma akayi wasairai da shi inda gafiyoyi da beraye ke shagalin su shekaru 3 bayan haka, makarantar ta koma aiki a kan janareta.

Tare da biliyoyin Naira da ake ikirarin ana kashewa, an kiyasta cewa kimanin MW 16.5 na injinan da ake da su da kuma iskar Carbon Dioxide za a tattara, ta yadda za a cire adadin megawatts na man fetur da injinan dizal ke cinyewa.

Abin takaici har yanzu Jami’ar Bayero Kano tana kashe sama da Naira miliyan 50 a duk shekara wajen samar da wutar lantarki ga makarantar. Sadiya Umar, ba asalin sunan ba, daga sashen nazarin zamantakewar al’umma, ta koka ga jaridar solacebase cewa rashin hasken ke tilastawa yawancin dalibai a kodayaushe yin karatu a wajen makarantar.

“Muna shan bakar wahala sosai, yanzu dole idan mu nason yin karatu cikin kwanciyar hankali, ba za muyi la’akari da ɗakin karatu ba, maimakon haka, muna zuwa wuraren abokanmu a wajen makarantar.

Zancen Gaskiya.

Ziyarar da jaridar Solacebase tayi zuwa tsangayar Sadarwa, Ilimi, Kimiyyar zamantakewa, da kuma aikin injiniya, ya tabbatar da hakikanin abubuwan dake faruwa a jami’ar.

A Sashin Sadarwa ma Jami’a da Har ila yau, a sashin Nazarin Watsa Labarai, an ji sautin janaretansu na aiki a ko’ina cikin Makarantar. Sashen Ilimi, Injiniya, da Kimiyyar zamani, su ma duk abin dayane kamar yadda yake faruwa a yawancin sassan makarantar da janareta.

Amma ga azuzuwa da wuraren wasan kwaikwayo, ɗalibai da yawa suna yin amfani da mafificin hannu don samar da iska mai dadi saboda zufa da zafi don samun iska yayin da laccoci ke gudana.

A cikin ɗakin karatu na makarantar, ɗalibai na yin karatu a cikin yanayi mai zafi yayin da dare janareta na ɗakin karatu ke aiki daga 6 na yamma zuwa 8 na yamma.

Dalibai irin su Amos Danlami da aka ga suna ta kaiwa-da-kawowa a dakin karatu sun bayyana cewa sun saba da yanayin. “Bana damuwa da zafi, kawai na sanya lokacin karatuna ne.

Kafin kaddamar da cibiyar hasken rana a shekarar 2019, bayanai da wannan jarida ta samu ya nuna cewa a shekarar 2018, an amince da jimillar naira miliyan 26,965,338 don amfani dasu a wutar lantarki, sannan an amince da miliyan 20,398,785 na kudin man fetur da dizal na janareta. A shekarar 2019, a shekarar da aka kaddamar da aikin, an amince da samar da wutar lantarki akan kudi naira miliyan 26,965,338, yayin da 20,398,785 kuma aka amince a matsayin kasafin kudin sayen dizal da man fetur a makarantar.

A shekarar 2020, shekarar COVID-19, Naira miliyan 22,139,912 aka amince dasu wajan wutar lantarki, yayin da miliyan 57,800,977 aka amince dasu dan amfani da dizal, wanda ya ninka adadin kasafin kudin da aka amince da shi idan aka kwatanta da na shekarar 2019.

Wani abin sha’awa kuma shi ne, a shekarar 2021, adadin da aka amince da kasafin kudin man fetur ya karu zuwa miliyan 80,398,785 yayin da a bangaren wutar lantarki kuma an kiyasta adadin da ya kai miliyan 26,965,338.

Injiniya Haruna Aliyu, Injiniya ne mai kula da aikin hasken rana a wata hira da jaridar ta yi da shi ya kasa amsa dukkan tambayoyin sai dai ya bayar da kadan.

“Cibiyar makamashin hasken rana ta dade da daina aiki, bayan an gina ta tare da kula da ita da Hukumar Raya Wutar Lantarki ta Karkara (REA), amma daga baya aka mika ta ga makarantar kuma sun mika ta gaba daya. “Kamfani ne na kasar Jamus wanda shike aiwatar aikin ya ki zuwa ya taimaka wajen warware matsalolin, inda suka bayyana rashin tsaro a matsayin babban abin da ya sa suka ki amincewa zuwa makarantar dan shawo kan matsalar.

Engr. Dan Umma, Daraktan Sashen Kulawa da kadarori na Jami’ar Bayero Kano da aka tuntube shi ta wayar tarho ya ki amsa tambayoyi, inda ya umurci dan jaridar da ya fara neman izini daga Shugaban Jami’ar kafin ya amsa duk wata tambaya dangane da aikin hasken rana.

Daraktan hulda da jama’a na cibiyar ana bangare Lamara Garba yayin da yake bayar da cikakken bayani kan halin da masana’antar sarrafa hasken rana ke ciki ya danganta ruwan sama a matsayin musabbabin barnar, inda ya ce makarantar kuma ba ta da adadin kudin da za ta gyara ta.

“Mun gano cewa injin ne ya lalace kuma zai kashe kudi wajen gyarawa. “Kamfanin yana ba da dalilai da yawa da ya sa ba za su iya zuwa Afirka a yanzu ba, amma a yanzu makarantar tana kan tattaunawa don ganin an magance matsalar da kamfanin na Jamus,” in ji Garba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here