Gwamnatin Kano ta gargaɗi makarantun kuɗi kan ƙarin kuɗin makaranta ba tare da izini ba

Abba Kabir Yusuf Yusuf 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta yi gargaɗi ga mamallaka makarantun kuɗi da su guji ƙara kuɗin makaranta ba tare da samun sahalewar hukuma ba.

Sakataren hukumar kula da Makarantun kuɗi da na sa-kai ta Jihar Kano, Malam Baba Umar, ya bayyana haka a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) a Kano.

Ya ce doka da ta kafa hukumar a shekarar 2014 ta tanadi cewa duk wani ƙarin kuɗin makaranta dole ne gwamnati da kuma ƙungiyar iyaye da malamai (PTA) na makarantar su amince da shi kafin aiwatarwa.

Karin labari: Tinubu ya naɗa Bunkure a matsayin shugaban Jami’ar Tarayya ta Zariya, ya naɗa Nakore da Kodage a majalisar gudanar a Jami’ar ilimi ta tarayya a Kano

Ya ƙara da cewa duk wata makaranta da ta karya wannan doka za ta fuskanci hukunci.

Haka kuma ya gargadi masu makarantu da su daina tilasta wa iyaye sayen littattafai, kayan makaranta, riga mai kauri (cardigan), ko wasu kayayyaki kai tsaye daga makaranta, musamman waɗanda ba su da alaka kai tsaye da karatu.

Umar ya bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da sa ido wajen tabbatar da bin doka, sai dai ya jaddada cewa ba za a yi amfani da wannan iko wajen tsoratar da masu makarantu ba.

Ya kuma shawarci iyaye da su rika bincika idan an amince da karin kuɗi kafin su biya, tare da ƙarfafa su da su rika biyan kuɗin makaranta akan lokaci domin sauƙaƙa gudanar da ayyukan makarantu yadda ya dace.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here