Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci kwamitin majalisar zartarwa ta tarayya da ya hanzarta ɗaukar matakai domin rage farashin abinci a faɗin ƙasar.
Ministan Jiha na Aikin Gona da tsaron Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya bayyana haka a Abuja ranar Laraba.
Ya ce umarnin ya shafi tabbatar da ingantaccen jigilar kayan gona a hanyoyi don rage kuɗin sufuri.
Abdullahi ya ce shugaban ƙasa ya na da burin cimma ikon cin abinci wanda ƙasar nan da kanta ke samarwa (food sovereignty), ba wai kawai samun isasshen abinci ba, har ma da tabbatar da cewa ana iya siya cikin sauƙi, ana iya samu a ko’ina, kuma abincin na ƙunshe da sinadaran gina jiki da za a iya dogaro da shi.
Karin labari: Majalisar Dattijai: Kudirin kafa hukumar bunkasa noman shinkafa ta kasa ya tsallake karatu na biyu
A cewarsa, gwamnati za ta ƙaddamar da shirin kula da lafiyar ƙasa ga manoma domin ƙara yawan amfanin gona, tare da sabunta tsarin ƙungiyoyin haɗin gwiwa na manoma domin samun albarkatu da kuma ƙarfafa manoman karkara.
Ministan ya ƙara da cewa shugaban ƙasa na da matuƙar sha’awa ga ƙungiyoyin haɗin gwiwa saboda rawar da suke takawa wajen tara albarkatu, samar da ayyukan tattalin arziƙi, da inganta rayuwar mambobinsu.
Ya kuma tunatar da cewa a baya, Tinubu ya bayyana a ranar Dimukradiyya cewa Najeriya tana kan hanyar cimma ikon cin abinci da kanta ta hanyar matakan da gwamnatin sa ta ɗauka, inda ya jaddada manufar sa na ƙarfafa masana’antu da samar da ci gaban tattalin arziƙi mai dorewa.










































