Tsohon shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, ya sake jaddada cewa yana da cikakken biyayya ga tsarin gaskiya da rikon amana, tare da kira ga ‘yan Najeriya su taka rawar gani wajen ganin ƙasar ta ci gaba.
Kyari ya bayyana haka ne bayan ya amsa gayyatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta yi masa a Abuja ranar Laraba.
Karin ya isa ofishin hukumar da misalin ƙarfe 1 na rana, ya kuma fita da misalin ƙarfe 9 na dare.
A cewarsa, zuwansa ya nuna yadda yake girmama doka da bin tsarin gaskiya na ƙasa.
Labari mai alaƙa: Yanzu-yanzu: Mele Kyari ya bayyana a Hedikwatar EFCC
Ya ce ya yi nasa ɓangaren wajen bautawa ƙasa, yanzu kuma aikin hukumar EFCC ne ta yi nata cikin gaskiya da adalci.
Kyari ya kara da cewa ya yi shekaru 34 yana hidima a NNPC da NNPCL, daga ciki shekaru 17 yana rike da mukaman shugabanci, musamman cikin shekaru 5 da watanni 9 na ƙarshe.
Ya ce wannan aiki bai bashi damar hutun makonni biyu ma ba, sai yanzu bayan an rusa shugabancin hukumar.
Ya bayyana cewa ya yi hidimar ƙasar ne da tsoron Allah, kuma yana shirye ya bada hisabi a kowane lokaci domin ya san idan bai bada hisabi ga mutane ba, to tabbas zai bada hisabi a gaban Allah.
Kyari ya kuma gargadi kafafen yaɗa labarai da su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba, saboda hakan na iya haifar da mummunar fahimta ga masu zuba jari da al’ummar ƙasa baki ɗaya.
Ya gode wa dangi da abokai da suka nuna damuwa, tare da tabbatar musu cewa yana nan a shirye ya amsa duk wata tambaya ta doka da aka yi masa.













































