Shugaba Tinubu zai yi jawabi ga shugabannin duniya a taron Majalisar Dinkin Duniya

Bola Ahmed Tinubu 750x430

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai yi jawabi a gaban shugabannin ƙasashen duniya a zauren babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) karo na 80, wanda za a gudanar a hedikwatar MDD dake birnin New York, ranar Laraba, 24 ga Satumba.

Bisa ga jadawalin da aka fitar daga Majalisar, Tinubu zai yi jawabi a rana ta biyu na taron, da misalin ƙarfe 8:30 na dare agogon New York (ƙarfe 2:30 na rana agogon Najeriya). Za a sanya shi na 17 cikin jerin shugabannin da za su yi jawabi a waccan rana.

Karanta: Tinubu ya ba da sabon umarni don rage farashin abinci

Taron zai tattaro shugabanni 195 daga sassa daban-daban na duniya, ciki har da shugabannin ƙasashe 98, mataimakan shugaba 5, firamiyoyi 44, mataimakan firamiyan 4, ministoci 37, yarima guda ɗaya da shugabannin tawaga 4.

A bisa al’ada, shugaban ƙasar Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, zai fara jawabi, sannan ya biyo shi shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, kasancewar ƙasarsu ce mai masaukin baki.

Sai dai an bayyana yiwuwar sauyi a jadawalin idan Tinubu bai halarci taron da kansa ba.

A shekarar 2024, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya wakilci Tinubu, kuma ya yi jawabi a rana ta farko, abin da masana suka ce ya saba al’ada, amma ya samu ne saboda matsayin Najeriya a idon duniya da kuma dabarun diflomasiyya na jakadunta.

Babban jigon tattaunawar bana shi ne: “Mafi ƙarfi tare: Shekaru 80 da ƙari domin zaman lafiya, ci gaba da kare haƙƙin ɗan Adam.” An buɗe zaman karo na 80 a ranar 9 ga Satumba tare da naɗin Annalena Baerbock, tsohuwar Ministar Harkokin Waje ta Jamus, a matsayin shugabar taron.

Ita ce mace ta biyar a tarihin MDD da ta rike wannan mukami.

Bayan babban taron, za a gudanar da wasu muhimman taruka, ciki har da taron tunawa da cikar shekaru 80 da kafuwar MDD, taron ci gaban dorewa (SDG Moment), taron shekaru 30 na babban taron mata na duniya, taron kan Falasɗinu da mafita ta ƙasashe biyu, taron sauyin yanayi, da kuma kaddamar da tattaunawa kan tsarin mulkin mallakar fasahar AI a duniya.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here