Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta sake baiwa gwamnatin tarayya wa’adin awanni 24, tare da barazanar shiga yajin aikin gargadi na kasa baki daya daga ranar Juma’a, 12 ga Satumba, bayan karewar wa’adin kwanaki 10 da ta bayar a baya ba tare da samun sauyi ba.
Wannan matakin ya biyo bayan taron gaggawa da kungiyar ta gudanar a Abuja, inda aka amince da dakatar da aiki idan gwamnati ba ta biya bukatunsu ba.
NARD ta ce tun a watan Yuli ta baiwa gwamnati wa’adin makonni uku, daga bisani ta tsawaita domin tattaunawa, amma duk bai haifar da wani sakamako ba.
Daga cikin bukatun kungiyar akwai biyan kudin horon likitoci (MRTF) na 2025, biyan bashin watanni biyar na karin albashin CONMESS (25/35%), da kuma duk sauran hakkokin albashi da ake bin su.
Haka kuma, likitocin sun koka da rashin biyan lawus na 2024, rike takardun membobinsu daga National Postgraduate Medical College of Nigeria (NPMCN), da kuma rage darajar takardun kwalejojin likitoci na Afrika ta Yamma (MDCN).
Karin labari: NARD ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 10 kafin shiga yajin aiki saboda rashin biyan bukatunsu
A matakin jihohi, NARD ta zargi gwamnatin Kaduna da kin cika yarjejeniya da likitoci na asibitin Barau Dikko yayin da gwamnatin Oyo ta ci gaba da nuna sakaci ga walwalar ma’aikata a asibitin, Ogbomoso, inda likitoci ke kan yajin aikin da ba shi da iyaka.
Kungiyar ta sake jaddada bukatunta, ciki har da biyan duk hakkokin da suka rage, fara biyan alawus na musamman, bayar da takardun membobin NPMCN ba tare da bata lokaci ba, da kuma cikakken aiwatar da tsarin CONMESS 2024 musamman a jihar Kaduna.
Ta kuma bukaci gwamnatocin jihohi su baiwa walwalar likitoci muhimmanci domin dakile matsalar ficewar kwararru kasashen waje (brain drain) da tabbatar da zaman lafiya a fannin kiwon lafiya.













































