NARD ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 10 kafin shiga yajin aiki saboda rashin biyan bukatunsu

NARD

Kungiyar Likitoci ta Najeriya NARD, ta ba da sabon wa’adin kwanaki 10 ga gwamnatin tarayya da sauran hukumomin da abin ya shafa, inda ta yi gargadin shiga yajin aikin gama gari a fadin kasar idan har ba a biya bukatunta ba.

Kudurin yana kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban NARD, Dr. Tope Osundara da Babban Sakatare Dakta Oluwasola Odunbaku da Sakataren yada Labarai da hulda da Jama’a, Dakta Omoha Amobi, bayan wani gagarumin taron Majalisar zartarwa ta kasa E-NEC da aka yi ranar Lahadi.

Kungiyar ta tuna cewa tun farko ta bada wa’adin makonni uku a watan Yuli, kafin ta kara wa’adin da wasu makonni uku domin a ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki. Sai dai ta nuna rashin jin dadin ta kan yadda har yanzu gwamnati ba ta cika alkawuran da ta dauka ba.

A cewar NARD, yawancin likitoci masu neman ƙwarewa har yanzu ba a biya su ba don Asusun Horar da alawus na 2025 (MRTF). Har ila yau, ta yi fatali da gazawar da aka samu na biyan basussukan watanni biyar daga kaso 25-35 cikin 100 na Tsarin Albashin Lafiya, CONMESS, tare da sauran basussukan albashin da aka dade ana bin su.

Likitocin sun ci gaba da yin Allah wadai da rashin biyan kudin alawus na 2024, da kuma abin da suka bayyana a matsayin rashin adalci na rashin ba su takardun shaidar zama mamba na kwalejojin likitoci da kasashen yammacin Afirka da kungiyar likitoci na hakori ta Najeriya (MDCN) ta yi.

Za mu fara gudanar da aikin kula da marasa lafiya kyauta ƙarƙashin NEMSAS- AKTH

Sun kuma nuna rashin gamsuwa da jinkirin da aka samu na bayar da shaida ga wadanda suka yi nasara a Kwalejin Kiwon Lafiya ta Najeriya, NPMCN.

Dangane da batutuwan da suka shafi matakin jiha, NARD ta soki gwamnatin jihar Kaduna kan yadda ta kasa cika yarjejeniyoyin da aka kulla da mambobinta a asibitin koyarwa na Barau Dikko, duk kuwa da sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna. Ta kuma zargi gwamnatin jihar Oyo da yin sakaci da jindadin likitoci a asibitin koyarwa na LAUTECH da ke Ogbomosho, inda ake ci gaba da yajin aikin da ba a san iyakar ba.

Yayin da yake yabawa jihohin da suka biya MRTF 2025, E-NEC ta bukaci gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi su dauki matakin gaggawa.

Daga cikin mahimman buƙatun su akwai biyan kuɗi na 2025 MRTF ga duk likitocin da suka cancanta, biyan bashin watanni biyar na CONMESS da sauran basukan albashi, Biyan alawus na 2024 da fara biyan tallafin ƙwararrun likitoci ga duk likitoci.

Sauran sun hada da dawo da karramawar shaidar zama memba a yammacin Afirka da MDCN ta yi, da gaggawar bayar da takardar shaidar zama memba da NPMCN da aiwatar da 2024 CONMESS a jihar Kaduna da magance matsalolin jin dadi a jihar Oyo.

Sanarwar ta jaddada cewa dole ne dukkan gwamnonin jihohi su ba da fifikon jin dadin likitocinsu domin dakile hijira da tabbatar da daidaiton masana’antu a fannin lafiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here