Hukumar Kula da Kashe Gobara da Shige da Fice ta Civil Defence (CDCFIB) ta kaddamar da mataki na gaba na tsarin daukar ma’aikata na 2023/2024 ga Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS).
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar din da ta gabata, Sakataren Hukumar, Ja’afaru Ahmed, ya sanar da cewa, ‘yan takarar da aka zaba za su samu gayyata ta lambobin waya da adireshinsu na imel.
Waɗannan gayyata za su ba da cikakkun bayanai don tantancewar jiki, tabbatar da takaddun shaida, da gwajin ƙwarewa, farawa daga Satumba 15, 2024.
Hukumar ta jaddada cewa ba a bukatar wasu kudade a kowane mataki na daukar ma’aikata. Tun da farko dai, hukumar ta ba da tabbacin cewa za a kammala daukar ma’aikata 2,500 ne a karshen watan Satumbar 2024.