Ambaliya: Duk da kudaden da gwamnatin tarayya ke bawa jihohi, sun kasa kula da ciboyin lafiya a arewa

Mazan Gudu Health Post C 1 750x430

Daga Halima Lukman

Arewacin Najeriya na fama da ambaliyar ruwa a ‘yan kwanakin nan, na baya-bayan nan dai an samu ambaliyar ruwa a jihar Borno da ta yi mummunar illa da ta kai ga asarar rayuka da lalata dukiyoyi.

Ba Borno kadai ba, jihar Bauchi ma ta sha fama da ambaliya tare da yawancin jihohin Arewacin Najeriya ba a bar su da barnar da ambaliyar ta yi ba.

A cikin wannan rahoto, SolaceBase ta yi nazari kan shirya-shiryen kiwon lafiya na jihohi don magance tasirin ambaliyar ruwa a cikin jihohi.

Wannan rahoto ya yi nazari kan yanayin cibiyoyin kiwon lafiya ganin cewa a cikin shekarar 2022 da aka yi ambaliyar ruwa da dama cibiyoyin kiwon lafiya sun lalace, wanda hakan ke nufin akwai cibiyoyin kiwon lafiya da za su taimaka wajen magance ambaliyar ruwa a shekarar 2022, yayin da aka yi watsi da su ta kara tabarbare hanyoyin samun lafiya ga wadanda ambaliyar ta shafa.

Tuni, a cikin 2024, ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar mutuwar mutane 259 a cikin jihohi 22 na kasar.

Bayanai daga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa sun nuna cewa mutane 35 ne suka mutu a Kano, 34 kuma a Jigawa.

Yayin da lamarin ambaliya a Borno ya banbanta, ganin cewa hatta cibiyoyin kiwon lafiya duk sun rushe.

Bita ya nuna cewa jihar Kano ta kashe Naira biliyan 5.1 a fannin kiwon lafiya a matakin farko a shekarar kasafin kudi na shekarar 2024, duk da haka, ta kashe Naira miliyan 88 ne kawai a cikin watanni shida na farkon shekarar 2024 don bukatun kiwon lafiya. Hakan ya zo ne bisa cikakkun bayanai daga takardar aikin kasafin kudin jihar.

Jihar Zamfara ta kasafta Naira biliyan 1.760 samar da cibiyoyin lafiya da asibitoci a shekarar 2024, amma har zuwa watanni shida na farkon shekarar, ba ta kashe wani kudi ba.

Gyaran asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya ya kai Naira biliyan daya, amma a cikin watanni shida na farkon shekarar, ba a kashe komai ba don wannan manufa, cikakkun bayanai kan takardun aikin kasafin kudi na jihar ya nuna.

A jihar Kogi, babban kasafin kudin hukumar kula da lafiya matakin farko ya kai naira miliyan 451 kacal ba tare da kashe komai ba a watanni shida na farkon shekarar.

Tuni dai masana ke fargabar cewa idan Najeriya ta ba da fifiko ga karancin samun kulawar kiwon lafiya, wasu da dama daga cikin ‘yan Najeriya na iya fuskantar illa sakamakon ambaliyar ruwa wanda ya sa yawancin wadanda abin ya shafa ke fafutukar kare rayukansu da kuma bukatar shiga tsakani.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here