
Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, ya ce matatar Dangote za ta fara rabon motocin man da ake kira Premium Motor Spirit (PMS), wanda aka fi sani da fetur, a ranar Lahadi.
Edun, wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar tara haraji ta tarayya (FIRS), Dr Zacch Adedeji, ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja ranar Juma’a.
Edun ya bayyana cewa, “Ina farin cikin sanar da cewa an kammala dukkan yarjejeniya kuma za a fara lodin kashin farko na PMS daga matatar Dangote a ranar Lahadi 15 ga Satumba.
Ya kuma kara da cewa daga ranar 1 ga Oktoba, NNPC Ltd. za ta fara samar da kusan 385kbpd na danyen mai ga matatar Dangote, wanda za a biya a Naira.
Kazalika, matatar Dangote za ta samar da PMS da dizal kwatankwacin darajar kasuwar cikin gida, wanda za a biya a Naira.
“Matatar Dangote za ta siyar da Diesel a Naira ga duk mai sha’awar sayen man. PMS za a sayar wa NNPC ne kawai, NNPC za ta sayar wa ‘yan kasuwa daban-daban a yanzu,” inji shi.
Edun ya ce duk kudaden da suka hada da (NPA, NIMASA, da sauransu) za a biya su a Naira.