Zaben Osun: Hukumar ICPC ta Kama Wasu da Ake Zargin Masu Sayen Kuri’u ne lokacin zabe

ICPC arrests suspected vote buyers in Osun election
ICPC arrests suspected vote buyers in Osun election

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta kasa ICPC, tace jami’anta dake sanya ido kan zaben gwamnan Jihar Osun, sun samu nasarar kama mutum 3 dake sayan kuri’u.

Mai magana da yawun hukumar Uwargida Azuka Ogugua, ce ta tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da fitar ranar Asabar a birnin tarayya Abuja.

Tace guda cikin wadanda aka kama din mai suna Dapo Olayode, an kama shi ne a mazabar Iremo a yankin Ife ta Arewa, dake santoriyar Osun ta gabas.

A cewar sanarwar Olayode an kama shi ne da jerin sunayen masu kada kuri’a tare kuma da kwace waya a hannunsa kirar android.

Ta kara da cewa an kuma kama wanda ake zargi da siyan kuri’u da jerin sunayen mutane 100 da ake tsammanin za a biya kowannensu Naira dubu 5,000.

Ogugua, ta ce duk da rauni da shugaban masu sayan kuri’ar ya samu a kokarin guduwa, amma hukumar ta samu nasarar kwace littafin da ke dauke da jerin sunayen masu kada kuri’a su 100.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here