Sanata Ali Ndume ya yi barazanar barin APC

Ali Ndume
Ali Ndume

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ce zai iya ficewa daga jam’iyyar APC idan har shugaba Bola Tinubu ya kasa gyara al’amura a kasar nan.

Sanata Ndume, ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da shi ta cikin shirin “Prime Time”, na gidan Talabijin din Arise, inda ya caccaki shugabaTinubu ya na mai cewa ya sha ganawa da yan jam’iyyun adawa da ke neman kafa wata hadaka.

Sanatan ya ce, har yanzu ya na ci gaba da kasancewa dan jam’iyyar ta APC amma bisa hakuri, da abubuwan da ke faruwa a cikinta tare da yakinin cewa shugaba Tinubu zai iya gyara Najeriya.

Haka kuma, Sanata Ali Ndume, ya soki dalilan da suka sa wasu suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here