Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda ya bayyana cewa auna nasarar aikin gwamnati yana danganta ne da irin tasirin da take yi ga rayuwar talakawa, inda ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na inganta tsaro, ci gaba da kuma gyaran hukumomi.
Ya bayyana hakan ne yayin bikin Sallah na shekarar 2026 da aka fi sani da Hawan Bariki, wanda aka gudanar a gidan gwamnati da ke Katsina a ranar Lahadi.
Bikin na durbar mai kayatarwa ya samu halartar jakadun ƙasashen Tarayyar Turai guda 17, sarakunan gargajiya, jami’an gwamnati da dubban jama’a, inda mahaya doki suka nuna al’adun gargajiya na jihar Katsina.
Gwamnan ya bayyana cewa bikin Hawan Bariki ba kawai shagali ba ne, illa yana wakiltar tarihi, asali da kuma haɗin kan al’ummar jihar, tare da tunatar da mutane muhimmancin darajoji irin su addini, mutunci, tausayi, jarumtaka da hidima.
Ya kuma nuna cewa halartar jakadun ƙasashen waje alama ce ta ƙarin amincewar duniya ga jihar Katsina da kuma al’adunta na zaman lafiya.
Dangane da tsaro, Radda ya ce gwamnatinsa ta ɗauki hanyoyi daban-daban na soja da kuma na al’umma wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi, ciki har da kafa rundunar sa-kai ta Katsina Community Watch Corps domin ƙarfafa tsaro a matakin ƙasa.
A ɓangaren ci gaba, gwamnan ya bayyana cewa an kammala muhimman ayyukan hanyoyi a Katsina, Funtua da Daura, tare da gina hanyoyin karkara domin taimaka wa manoma isa kasuwanni cikin sauƙi.
Ya ƙara da cewa ana rarraba tan dubu 40,000 na taki duk shekara a farashi mai sauƙi, tare da samar da fiye da taraktoci 400 a ƙananan hukumomi 34 na jihar domin bunƙasa noma.
A fannin ilimi da lafiya kuwa, ya ce an gina makarantu na zamani guda uku, an kammala makarantu sama da 85, sannan an ɗauki malamai fiye da 7,000 aiki, tare da kafa cibiyar dialysis ta zamani, cibiyar binciken lafiya da kuma gyara cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko sama da 250.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa an biya bashin fansho da ya haura naira biliyan 45, tare da ƙaddamar da tsarin dijital domin inganta aiki da gaskiya a harkokin gwamnati.
A nasa jawabin, Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir-Usman ya buƙaci al’umma su kasance masu biyayya ga doka, haɗin kai da kuma zaman lafiya, yana mai cewa ci gaba yana buƙatar haɗin gwiwa da mutunta juna.
Ya yaba da jagorancin gwamnan, yana mai cewa ingantacciyar gwamnati tana auna kanta ne da yadda take samar da tsaro, walwala da kuma fata ga al’umma, tare da gode wa jakadun ƙasashen waje bisa halartar bikin wanda ya nuna martabar al’adun Katsina.













































