Bauchi: MRA ta yi Allah-wadai da cin zarafin dan jarida, ta bukaci bincike cikin gaggawa da daukar mataki

Mr. Mohammed Adamu Albarka Radio journalist 1 750x430

Kungiyar kare ‘yancin kafafen yada labarai ta (MRA) ta yi Allah-wadai da rahoton dukan da jami’an ‘yan sanda suka yi wa wani dan jarida na Albarka Radio, Mohammed Adamu, a lokacin da yake rufe bikin Hawan Sallah a Bununu, hedikwatar karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar Bauchi.

Kungiyar ta bayyana lamarin a matsayin wani sabon hari da ba za a amince da shi ba kan ‘yancin ‘yan jarida da kuma tsaron su a Najeriya, tare da jaddada cewa irin wadannan abubuwa na kawo barazana ga aikin yada labarai.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a Lagos, MRA ta bukaci a gudanar da cikakken bincike cikin gaggawa da gaskiya kan lamarin, tare da tabbatar da hukunta dukkan jami’an ‘yan sandan da ke da hannu, da kuma ba dan jaridar diyya bisa raunukan da ya samu.

Rahotanni sun nuna cewa Mohammed Adamu yana wurin taron ne domin gudanar da aikinsa na jarida, inda jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin Baturen dan sanda Jamilu Kabir, suka tare shi yayin da yake kokarin shiga yankin da aka tanadar wa ‘yan jarida domin rufe taron.

Bayan ya nace kan hakkinsa na yin aikinsa, jami’an sun lakada masa duka da sanduna duk da cewa ya bayyana kansa a matsayin dan jarida, lamarin da ya janyo masa raunuka a kai tare da zubar jini, sannan aka kore shi daga wurin taron.

Daga bisani an kai shi asibiti domin samun kulawa, yayin da jami’in shirye-shirye na MRA, John Gbadamosi, ya bayyana cewa wannan lamari yana daga cikin ci gaba da cin zarafin ‘yan jarida a jihar Bauchi da ma fadin kasa, wanda ke tauye ‘yancin jama’a na samun bayanai.

Kungiyar ta kuma bukaci Babban Sufeton ‘yan sanda, Olatunji Disu, da ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike, gano dukkan wadanda ke da hannu, tare da daukar matakin ladabtarwa a kansu.

Sannan ta bukaci gwamnatin tarayya ta tabbatar da kare ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma tsaron ‘yan jarida a dukkan lokuta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here