Ibtila’in Gobara Singer: Sanata Barau ya ziyarci kasuwar, ya ba wa wadanda gobarar ta shafa tallafi Naira Miliyan 100

WhatsApp Image 2026 02 15 at 20.33.51 750x430

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya kai ziyarar jaje a Kasuwar Singer dake karamar hukumar Fagge ta Jihar Kano a ranar Lahadi, inda gobarar wuta ta hallaka kayayyaki da dukiyoyi masu darajar fiye da Naira Biliyan 5.

Sanatan, wanda Mai Ba shi Shawara na Musamman kan Harkokin yada Labarai, Malam Ismail Mudashir, ya fitar da sanarwa a ranar Lahadi, ya ce, Shugaban kasuwar, Alhaji Junaidu Zakari ne ya karbi tawagar tare da dubban ‘yan kasuwa da abin ya shafa, sannan ya ba wa wadanda gobarar ta shafa gudunmawar kuɗi na Naira Miliyan 100 domin rage radadin hasarar.

Yayin da yake jawabi ga ‘yan kasuwar, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya nuna matuƙar bakin ciki kan lamarin, inda ya ce wannan gobara ba ta shafi ‘yan kasuwar kawai ba, har ma da al’ummar Kano gaba ɗaya da ƙasar baki ɗaya.

Sanatan, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Farko a Majalisar kungiyar raya tattalin arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ya yi alkawarin tallafawa wajen samar da kayan aikin kashe gobara na zamani a kasuwar.

A cikin jawabin sa, Shugaban kasuwar, Alhaji Junaidu Zakari, ya bayyana cewa kasuwar ta fuskanci gobarar wuta guda biyu a ‘yan kwanakin baya, wanda ya janyo asarar kayayyaki da dukiyoyi masu darajar fiye da Naira biliyan 5.

Ya kuma nuna matuƙar godiya ga Sanata Barau bisa ziyarar ta’aziyya da goyon bayan da ya ci gaba da bayarwa.

Sanata Barau ya kasance tare da Ministan Harkokin Gine-gine da Ci gaban Birane, Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Ata, Kwamishinan Kano na Renewed Hope Initiative, Malam Salisu Sagir Takai, ‘Yan Majalisar Jihar Kano, Masu Ba da Shawara na Musamman, da sauran ma’aikata a ziyarar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here