Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umurci Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci wata babbar tawagar gwamnatin Tarayya zuwa jihar Kano sakamakon gobarar da ta auku a Kasuwar Singer a ranar Asabar.
Wannan umurni ya fito ne a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayar a ranar Lahadi a Abuja.
Tawagar za ta tashi daga Abuja a ranar Litinin domin isar da saƙon jaje ga ‘yan kasuwar da suka rasa Biliyoyin Naira a gobarar.
Gobarar, wadda ta fara ne da yamma ta Asabar har ta ci gaba har zuwa safiyar Lahadi, ta yi mummunar illa ga kasuwar.
Shugaban ƙasa Tinubu ya nuna bakin ciki saboda wannan lamarin shi ne karo na biyu da ya faru a wannan kasuwar cikin ƙasa da makonni biyu.
Tawagar za ta bayyana shirin bayar da tallafin kuɗi domin tallafawa wadanda abin ya shafa da kuma taimakawa jihar Kano wajen sake buɗe kasuwar cikin sauri.
Daga cikin mambobin tawagar akwai Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin. Sauran mambobi sun haɗa da Sanata Kawu Ismaila da Wakilin Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi, Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar Wakilai.
Haka kuma, Ministan Harkokin Jin Kai, Dr Bernard Doro, da Daraktan Janar na Hukumar Kula da Bala’o’i (NEMA), Hajiya Zubaida Umar, suna cikin tawagar.
Shugaban ƙasa ya riga ya yi magana ta wayar tarho da Gwamna Abba Yusuf don samun rahoton abin da ya faru.
Bugu da ƙari, Tinubu ya umurci gudanar da cikakken bincike kan musabbabin sake faruwar gobar kasuwanni.













































