Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana bakin cikin sa kan rasuwar jigo, Alhaji Shehu Yahaya, inda ya bayyana rasuwar sa a matsayin babban rashi ga Jihar Kano da ma kasa baki daya.
A cikin sakon ta’aziyyar da kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a Kano a ranar Lahadi, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayi Alhaji Shehu Yahaya a matsayin dan kasuwa da ya cimma nasarori wanda ya rayu rayuwa mai kyau cikin gaskiya, mutunci da sadaukar da kai wajen hidima wa al-umma ba tare da gajiyawa ba.
Gwamnan ya ce a duk tsawon rayuwarsa, Alhaji Shehu Yahaya ya kasance mai himma wajen cigaban al’ummar unguwar Dakata Kawaji a karamar hukumar Nasarawa da kuma inganta zaman lafiya, inda ya bar tarihi ba tare da son rai ba, jagoranci da taimakon al-umma.
“Rasuwar Alhaji Shehu Yahaya babban rashi ne ba ga iyalin sa kadai ba, har ma da al’ummar Jihar Kano baki daya. Mun rasa uba, dan kasuwa mai Daraja kuma dan kishin kasa wanda za a ci gaba da tunawa da gudunmawar sa ga al-umma,” in ji Gwamna Yusuf.
Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya gafarta wa marigayin kurakuran sa, ya ba shi Aljannatul Firdausi, ya kuma ba iyalin sa, masoya da al’ummar Jihar Kano hakuri da juriyar daukar wannan babban rashi.
Marigayin ya bar ‘ya’ya da dama daga ciki akwai Inginiya Muhammad Shehu babban manajan Gerawa Group of Companies.











































