‘Yan Majalisar APC 192 Na Shirin Ficewa Daga Jam’iyyar

National assembly abuja building e
National assembly abuja building e

Kwamitin tsare-tsare na kungiyar yakin neman zaben Tinubu ya sanar da jam’iyyar APC cewa akwai yiyuwar ‘yan majalisar wakilai kusan 192 su fice daga jam’iyyar zuwa wasu jam’iyyu biyo bayan sakamakon zaben fidda gwani na jam’iyyar da ya sanya wasu mambobin jam’iyyar suka rasa tikitin komawa kujerunsu.

Kwamitin wanda tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal ke jagoranta, ya bayar da wannan masaniyar ne a cikin ‘Rahoton tabbatar da shugabancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a babban zabe mai zuwa na 2023.

Kwamitin wanda ya bayyana abubuwan da ya kamata jam’iyyar ta yi la’akari da su wajen ganin ta tsayar da dan takara da kuma zabin da jam’iyyar za ta iya, ta tuntubi shugaban kasa Muhammadu Buhari da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Bola Tinubu da shugabannin majalisar dokokin kasar da sauran shugabannin jam’iyyar kan su shiga tsakani, inda kwamitin ya kuma yi gargadin cewa ficewar ‘ya ’yan jam’iyyar na iya shafar nasararta a zaben 2023.

Rahoton ya ce kwamitin ya yi zama sau da dama a watan Yuni inda ya tattauna kan batutuwan da suka shafi abokin takara, tare da la’akari da addini.

Kazalika mambobin kwamitin sun yi wani kwarya-kwaryar jin ra’ayoyi daga masu ruwa da tsaki na addini da na siyasa da sauran jama’a, kuma sun yi amfani da tsarin al’adar addini daga jihohin Arewa 19 da kuma Babban Birnin Tarayya.

Dangane da batun dan takarar, kwamitin ya yi nuni da cewa, tikitin tsayawa takara na musulmi da musulmi da kuma na musulmi da kirista na da fa’ida matuka, sai dai ya yi gargadin cewa shiyya da addinin dan takara wasu batutuwa ne masu muhimmanci da ke bukatar yin nazari sosai.

Kwamitin ya ce tikitin takarar musulmi da kirista zai dore da daidaiton addini a tikitin takarar shugaban kasa tun kuma haka ake yi tun daga shekarar 1999 wanda hakan ne ake ganin zai iya kawo wa jam’iyyar nasara domin zai gamsar da kiristoci a shiyyar Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas.

Sai dai ta yi gargadin cewa Musulmin yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas na iya kada kuri’ar zabensu ga ‘yan takarar Arewa na jam’iyyun NNPP da PDP, kuma hakan na iya haifar da babbar asara ga jam’iyyar APC.

Duka dai kana batun Muslum-Muslum din, kwamitin ya ce zai taimaka wajen kawar da karfin kada kuri’a na jam’iyyun PDP da NNPP da kuma gamsar da al’ummar Musulmi wadanda ke da karfin kada kuri’a da za su iya tabbatar da nasara.

Sai dai kuma dangane da illar wannan haduwar, kwamitin ya ce bai kamata a yi watsi da rashin tabbas na sakamakon da za a iya samu ba, domin hakan zai haifar da rarrabuwar kawuna ga masu kada kuri’a ta hanyar addini.

A halin da ake ciki, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal, ya fito fili ya nuna adawa da zabin da Tinubu ya yi na cewa dan uwansa Musulmi ne a matsayin abokin takararsa.

Ya ce tunda jam’iyyar APC ta mika sunan Kashim Shettima ga hukumar INEC, al’ummar Kirista musamman a yankin Arewa za su nuna adawa bisa mayar da su saniyar ware a Siyasance.

Da yake bayyana rashin jin dadinsa ga Tinubu a wani sakon da ya aike wa daya daga cikin wakilan kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ta manhajar WhatsApp a daren ranar Juma’a, Lawal ya ce, “Na fada: Tinubu ya jefa kunci a zukataan kiristoci. Ya mika sunan Alhaji Kashim Shetima a matsayin wanda zai rufa masa baya a zaben shekarar 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here