Wani Babban Lauyan Najeriya, Mista Yakubu Chonoko Maikyau, ya zama shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) na 31.
Maikyau, ya lashe zaben da aka gudanar daga Safiyar ranar Asabar zuwa dare, inda ya samu kuri’u dubu 22 da 342.
Ya samu nasarar ne bayan doke abokan takararsa biyu, Messrs Joe-Kyari Gadzama mai mukamin SAN, da kuma Jonathan Taidi, tsohon babban sakataren kungiyar ta NBA.
“An kada kuri’u dubu 34 da 809 wanda Ya kai kashi 58 da digo 61 na yawan wadanda suka cancanci kada kuri’a, yayin da kuri’u dubu 1 da 314 suka lalace,” in ji shi.
Ya ce Maikyau ya samu kuri’u dubu 22 da 342 wanda ke wakiltar kashi 64 da digo 6 na kuri’un da aka kada, yayin da Gadzama ya samu kuri’u dubu 10 da 842, shi kuma Taidi ya samu kuri’u dubu 1 da 380.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya ruwaito cewa sauran wadanda suka yi nasara a zaben sun hada da Uwargida Linda Bala a matsayin mataimakiyar shugabar NBA ta farko da jimillar kuri’u dubu 21 da 717 da ke wakiltar kashi 66 da digo 3 na kuri’un da aka kada.
An zabi Mista Clement Ugo, ne mataimakin shugaban NBA na biyu da kuri’u dubu 11 da 377 wanda ya kai kashi 38 da digo 6 na kuri’un da aka kada a ofishin.
Uwargida Amanda Demechi-Asagba, shugabar kungiyar lauyoyin mata ta Afirka, ta zama mataimakiyar shugabar NBA ta uku da kuri’u dubu 19 da 602 da ke wakiltar kashi 64 da digo 6 na kuri’un da aka kada a ofishin.
Mista Adesina Adegbite ya lashe zaben ofishin babban sakataren NBA da jimillar kuri’u dubu 18 da 536 da ke wakiltar kashi 56 da digo 2 na kuri’un da aka kada ofishin.
Mista Daniel Kip ya zama mataimakin babban sakataren NBA da jimillar kuri’u dubu 10 da 71 da ke wakiltar kashi 31da digo 7 cikin 100 na kuri’un da aka kada a kujerar.
An zabi Uwargida Caroline Anze-Bishop matsayin Ma’ajin NBA da jimillar kuri’u dubu 12 da 12 da ke wakiltar kashi 37da 4 na kuri’un da aka kada a ofishin.
Ms Chinyere Obasi ta zama Sakatariyar jin dadin Yan kungiyar ta NBA da jimillar kuri’u dubu 10 da 452 da ke wakiltar kashi 32 da digo 4 na kuri’un da aka kada a ofishin.
An kuma zabi Mista Habeeb Lawal, a matsayin Sakataren Yada Labarai na NBA da kuri’u dubu 17 da 650 wanda ke wakiltar kashi 53 da digo 5 na kuri’un da aka kada a ofishin.
Mista Charles Ajiboye ya lashe zaben ofishin mataimakin sakataren yada labarai na da kuri’u dubu 17 da 811 da ke wakiltar kashi 57 da digo 1 na kuri’un da aka kada na ofishin.
Kamfanin dillancin Labarai na Kasa NAN ya ruwaito cewa an gudanar da zaben ne ta hanyar amfani da na’urar Computer.
Maikyau ya gaji Mista Olumide Akpata da aka zaba a shekarar 2020.
Akpata ya kafa tarihi a matsayin shugaban NBA daya tilo a cikin shekaru 10 da suka gabata.













































