Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wata mai suna Opoola Mujidat, da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a jihar Legas.
An kama ta ne bayan hukumar ta kama wasu fasinjoji biyu da ke tafiya Oman a ranar Litinin, 11 ga Yulin shekarar da muke ciki ta 2022.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi, ta ce an kama fasinjojin biyu, Raji Babatunde Kazeem da Akinbobola Omoniyi kafin su hau jirgi.
“Fasinjojin, Raji Babatunde Kazeem da Akinbobola Omoniyi, suna tafiya tare zuwa kasar Oman dake Gabas ta Tsakiya a cikin jirgin kasar Habasha a ranar Litinin 11 ga watan Yulin shekarar na n ta 2022 inda jami’an NDLEA suka tare su a filin jirgin. A binciken da aka yi a cikin jakunkunan su, an gano kullin tabar wiwi da aka boye a cikin wata jaka dauke da kayan abinci, wanda Kazeem ke dauke da ita.”
“Nan da nan Kazeem da Omoniyi suka sanar da jami’an yaki da miyagun kwayoyi cewa Mujidat da ke kusa da wurin ce ta ba su jakar da ke dauke da haramtattun kayan a filin jirgin, nan take kuma aka kama ta.”
A cewar sanarwar, Mujidat ta yi ikirari cewa ta kawo kayan ne da nufin fasinjojin biyu su bawa mijinta dake can a kasar Oman din.
Hukumar NDLEA ta ce ta kuma kama wani mutum mai suna Ernest Ojieh mai shekaru 52 a ranar 9 ga watan Yuli dauke da buhunan tabar wiwi sama da 91, masu nauyin kilogiram dubu 1 da 29 da digo 5 da aka boye a cikin wata babbar mota a garin Lafia na jihar Nasarawa.
A cewar hukumar, kamen ya zo ne kwana hudu bayan da jami’an tsaro a Agwan Doka dake Lafia, suka kama manyan buhuna guda 38 masu nauyin kilogiram 367, tare da kama wasu mutane biyu, Abdullahi Iliyasu, mai shekaru 30, da Bashir Mohammed, mai shekaru 29.
Hukumar ta kara da cewa, “A Kaduna da Adamawa, an kama sama da alluran kwayoyi na opioids, tare da cafke wadanda ake zargi a samamen da aka yi a jihohin biyu. A Kaduna kadai, an kama kwayoyin Tramadol da Diazepam guda dubu 294, da 400 daga hannun: Shaban Nasir da Aminu Usman da Shamsudeen Hussaini, da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma Sa’idu Yahaya da Umar Abubakar, a wani samame da aka gudanar a Kano, duk a ranar Juma’a 15 ga Yulin da muke ciki na 2022.
“Hakazalika, an kama sama da nau’i dubu 227,000 na Tramadol a wani samame da aka kai a wani kantin sayar da magunguna da ke Sabon Layi, kusa da babbar kasuwar Mubi, a karamar hukumar Mubi ta Arewa, dake Jihar Adamawa a ranar Lahadi 3 ga watan Yuli.













































