Rundunar ‘Yan sanda ta amince da yiwa Jami’ai Dubu 20 da Doriya Karin girma

IGP Usman Baba 1 678x381 1
IGP Usman Baba 1 678x381 1

Babban Sifetan Yan sanda na Kasa Usman Alkali Baba, ya amince da karawa kananan jami’an Yan sanda dubu 21 da 39 girma, wadanda rabonsu da samun karin girma tun a shekarar 2017.

Mukaddashin mai magana da yawun rundunar na Kasa CSP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana haka ranar Alhamis a Abuja.

Yace kananan jami’an da za a karawa girman daga mukamin Sajan zuwa Sifeto su dubu 20 da 572 ne, yayin da jami’ai 324 kuma za a yi musu karin girma daga mukamin Kofural zuwa Sajan, sai kuma Kurata 143 zuwa mukamin Kofural.

Adejobi yace karin girman wani bangare ne na yunkurin da ake yi wajen tabbatar da walwalar jami’an Rundunar.

Ya kara da cewa babban Sifetan Yan sanda Usman Alkali Baba, ya bada tabbacin za a ci gaba da karin girma akan lokaci ga jami’an da suka cancanta.

A cewar mai magana da yawun Rundunar karin girman zai karawa jami’an kwarin gwiwar jajurcewa akan ayyukansu.

Yace Rundunar ta kuma yi hadin gwiwa da hukumar Yan sanda ta kasa domin yiwa manyan jami’ai karin girma.

Adejobi, ya kara da cewa Babban Sifetan ya bada tabbacin cewa nan bada jimawa ba za a fitar da sunayen Manyan Jami’an da za a yiwa karin girman.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here