Rikicin Masarauta: Lauyoyi a Kano sun janye kare shari’ar Aminu Ado Bayero a kotu

Aminu Ado Bayero, Rikicin, Masarauta, Lauyoyi, Kano, janye, kare, shari'ar, kotu
A ranar Alhamis ne Mista Abdul Muhammed SAN da sauran lauyoyin Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado-Bayero, a rikicin masarautar Kano da ke ci gaba da...

A ranar Alhamis ne Mista Abdul Muhammed SAN da sauran lauyoyin Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado-Bayero, a rikicin masarautar Kano da ke ci gaba da yi, suka janye shari’ar da suke yi a gaban Babbar Kotun Jihar.

Wadanda suka shigar da karar sun hada da Babban Lauyan Jihar Kano da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano da kuma Majalisar Dokokin Jihar, ta bakin Lauyan su Ibrahim Isah-Wangida, ya shigar da kara mai kwanan wata 27 ga watan Mayu.

Karin labari: Wasu fusatattun matasa sun bankawa ofishin INEC wuta a Benue

NAN ta rawaito cewa a ranar 27 ga watan Mayu ne kotun ta bayar da umarnin dakatar da sarakunan da suka gabata a matsayin daina amsa sunan sarakuna domin samun zaman lafiya a Kano.

NAN ta rawaito cewa majalisar dokokin jihar a ranar 23 ga watan Mayu, ta rusa dukkan sabbin masarautun jihar guda hudu da aka kafa a jihar sannan Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sake nada Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sabon sarkin Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here