Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi barazanar sanya takunkumi ga bankunan ajiyar kudi (DMBs) da suka ki amincewa da yanke takardar kudin Naira.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa a ranar Alhamis mai dauke da sa hannun Solaja Olayemi, mukaddashin daraktan sashen hada-hadar kudi na CBN.
Babban bankin ya ce an samu rahotanni da dama a kan bankunan.
“Babban Bankin Najeriya (CBN) ya samu rahotanni da dama na kin amincewa da gurbatattun takardun kudin Naira da wasu bankunan Deposit Money (DMBs) suka yi,” in ji bankin.
Karin labari: Rikicin Masarauta: Lauyoyi a Kano sun janye kare shari’ar Aminu Ado Bayero a kotu
“Saboda haka, ya zama wajibi a tunatar da DMB cewa har yanzu dokar CBN mai kwanan wata 2 ga watan Yuli, 2019, mai lamba COD/DIR/GEN/CIR/01/006, wanda ta tanadi hukunci kan kin amincewa da takardar kudin Naira, har yanzu tana aiki.”
Babban bankin ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen sanya takunkumi mai tsauri kan bankunan da aka samu sun ki amincewa da ajiyar Naira daga jama’a, ta kowace hanya.
Har ila yau, a ranar 2 ga watan Yuli, CBN ya gargadi bankuna da dillalan kudaden kasashen waje da aka ba da izini kan kin amincewa da tsofaffin silsila da kananan daloli.
Karin labari: Ma’aikatan Najeriya sun bayyana takaicinsu kan karin kudin wutar lantarki
Babban bankin ya ce dole ne dukkan bangarorin da abin ya shafa su bi umarnin, yana mai jaddada rashin amincewa da karbar kudaden ajiya.
Babban bankin na CBN ya ce ya gano tsofaffin daloli har yanzu ana watsi da su yayin binciken kasuwar masu amfani.