An samu rudani game da batun sauya sheka na Manir Muhammad Dan’iya, mataimakin gwamnan jihar Sokoto.
A ranar Alhamis ne wata wasika da aka rawaito Dan’iya ya mika takardar ficewa daga jam’iyyar PD taketa yawo a shafukan sada zumunta.
A cikin wasikar wacce daya daga cikin hadiman mataimakin gwamnan ya tabbatar da cewa Dan’iya ya sanar da shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Kware da ke karamar hukumar Kware a Sokoto kan sauya shekarsa.
Wasikar ta kasance kamar haka: “Na rubuto ne domin in sanar da ku ficewa ta daga jam’iyyar PDP daga ranar 8 ga watan Fabrairun 2023.
“Na yaba da damar da aka ba ni, wanda ya sa na yi aiki a wurare daban-daban a karkashin PDP,” ya rubuta.
Amma bayan sa’o’i, Aminu Abdullahi Abubakar, mai magana da yawun mataimakin gwamnan ya shaida wa Aminiya cewa har yanzu shugaban nasa na nan a jam’iyyar PDP.
Daga bisani ya fitar da sanarwa kan lamarin.
“An jawo hankalinmu gameda wata takarda da aka ce an fitar a Sakkwato cewa Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato Hon. Manir Dan’iya ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar PDP.
“Wannan ba gaskiya ba ne, kuma karairayi ne. Hon. Manir Dan’iya har yanzu dan jam’iyyar PDP ne mai kishin kasa, wanda ya kara tabbatar da biyayyarsa da goyon bayansa,” in ji Abubakar.
A halin da ake ciki, a taron gangamin jam’iyyar APC da ke gudana a Sokoto, Sanata Aliyu Wammakko, shugaban jam’iyyar APC a jihar ya bayyana cewa Dan’iya ya koma APC.
Ya ce mataimakin gwamnan yanzu yana tare da jam’iyyar kuma zai yi kokarin ganin ta samu nasara a zaben.
Sai dai Dan’iya baya cikin wadanda suka sauya sheka da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tarbe su zuwa APC.
Mataimakin gwamnan shine dan takarar sanata na jam’iyyar PDP a shiyyar Sokoto-Arewa. Ya yi yunkurin maye gurbin Gwamna Aminu Tambuwal amma Gwamnan ya nuna goyon bayansa ga Sa’idu Umar, tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, wanda a karshe ya zama dan takarar PDP.
Tambuwal shine Darakta Janar na yakin neman zaben Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar a zaben.













































