Shugaban jam’iyyar (NNPP) na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa yana iya komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne kawai idan aka cika wasu muhimman sharuɗɗa da ke tabbatar da mutunta tafiyar Kwankwasiyya.
Kwankwaso ya yi wannan bayani ne a gidan sa da ke Kano, lokacin da ya karɓi ziyara daga Buhari Bakwana, tsohon mai ba wa tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje shawara, tare da wasu jiga-jigan APC daga ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Ya ce, a shirye yake ya tattauna da APC, amma sai an tabbatar da cikakkiyar girmamawa da amincewa ga tafiyarsa ta Kwankwasiyya.
Ya jaddada cewa ba zai taɓa watsar da mabiyansa ba saboda kowace yarjejeniya ta siyasa.
A cewarsa, shi da magoya bayansa sun taka muhimmiyar rawa wajen kafa APC, amma duk da wahalhalu da tsangwama daga hukumomin tsaro da suka sha, ba su samu yabo ko kulawa daga gwamnatin jam’iyyar ba a lokacin mulkin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.
Kwankwaso ya kuma zargi jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da irin wannan wulakanci lokacin da suka nemi komawa cikin ta, inda har ba su samu mukamin shugaban jam’iyya na shiyya ba.
Wannan, a cewarsa, ya ƙarfafa Kwankwasiyya wajen riƙe kai da kafarsu a siyasar Najeriya.
Kwankwaso ya ƙara jaddada cewa idan PDP ma ta zo domin tattaunawa, dole ne ta fara amincewa da kura-kuran da ta yi a baya, sannan ta gabatar da yarjejeniya a fili da kowa zai shaida, domin tabbatar da gaskiya da ɗorewar amana.












































