Sarkin Ilorin Sulu Gambari ya naɗa sabon Balogun Ajikobi a masarautar

Emir of ilorin

Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya naɗa Alhaji Suleiman Omokayode Abdulwahab a matsayin sabon Balogun Ajikobi na masarautar Ilorin, wanda shi ne na 13 a jerin masu rike da wannan mukami.

A cewar wata sanarwa da mai taimaka wa Sarkin, Dakta Abdulraheem Muritala, ya fitar a daren Juma’a, ya ce wannan naɗin ya biyo bayan rasuwar Balogun Ajikobi na 12, Alhaji Isiaka Yusuf Okunrinjeje, wanda ya rasu a ranar 23 ga Fabrairu, 2025.

Kafin wannan naɗi, Alhaji Suleiman ya yi aiki a matsayin Hakimin Ipaye tun daga ranar 10 ga Mayu, 2019, inda ya yi fice wajen gudanar da shugabanci da hidima ga al’umma.

Sanarwar ta bayyana cewa a matsayin wani sauyi na wucin-gadi, sabon Balogun zai ci gaba da kula da al’amuran masarautar Ipaye har sai an naɗa sabon hakimi a can.

Sarkin Ilorin ya yi addu’ar fatan alheri da nasara ga sabon Balogun Ajikobi, tare da roƙon Allah ya ba shi dogon rai, lafiya da hikima domin gudanar da nauyin manyan mukaman da aka ɗora masa cikin nasara.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here