ASUU ta bukaci a yi amfani da tsarin UTAS wajen biyan hakkokinsu

DF5E9ECC A853 4D89 B289 E0278627B6D9
DF5E9ECC A853 4D89 B289 E0278627B6D9

Kungiyar malaman jami’a ta kasa ASUU ta bukaci gwamnatin tarayya da tayi amfani da tsarin UTAS wajen biyan su bashin da suke bin gwamnati tare da sauran hakkokin su.

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin tarayya ta biya ‘ya’yan ta albashin da suke bi har na tsahon watanni 22, wanda aka ki biyan su sakamakon kin yadda da tsarin IPPIS.

Shugaban kungiyar ta ASUU shiyar Calabar Dakta Aniekan Brown ne ya bayyana yayin tattaunawa da manema labarai, inda ya ce mambobin kungiyar suna cikin matsanancin hali sakamakon rashin samun albashi fiye da watanni 22.

Ya bayyana cewa wannan sune kadan daga cikin dalilan da suka sanya kungiyar ke shirin shiga yajin aiki.

Ya bukaci gwamnatin tarayya tayi gaggawar cika alkawuran da ta daukar musu, idan ba haka ba babu abinda zai hana su shiga yajin aiki.

Dakta Aniekan Brown shine yake jagorantar kungiyar ASUU shiyar Calabar wadda take dauke da Jami’ar gwamnatin jihar Abia da Jami’ar gwamnatin jihar Akwa-Ibom da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta jihar Cross River sai Jami’ar gwamnatin jihar Ebonyi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here