Mai bawa Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguna ya bayyana sunan kungiyoyin addini gudu 3 masu taimakawa ‘yan ta’adda a Nigeria dama sauran kasashe dake yankin Sahel.
Manjo Janar Babagana Mongunu mai ritaya ya bayyana hakan ne a wajen taron kungiyar malamai da masu wa’azi da limamai na kasashen dake yankin Sahel wanda ke gudana a Abuja.
Ya ce kungiyar Boko Haram da ISWAP sune manyan kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka dade suna barazana ga rayuka da dokiyoyin al’ummar yankin Arewa maso yammacin Nigeria.
Ya kara da cewa akwai wata kungiya mai suna Islamic State in Greater Sahara (ISGS) wadda ke addabar yankin jamhuriyar Niger da Burkina Faso.
A cewar sa karuwar ayyukan kungiyoyin Jama’at Nasr al-Islam Wal Muslimin (JNIM) da Islamic and Muslim Support Group yana babbar barazana ga kasashen Africa.
Ya bayyana cewa ayyukan wannan kungiyoyi ya janyo asarar dubunnan rayuka tare da asarar dumbin dukiya.
Babagana Munguno ya yi kira da a samu hadin kai tsakanin gwamnatoci fa malaman addini domin shawo kan matsalar da karuwar kungiyoyin ta’adda a Africa.













































