Yanzu-yanzu: Gawuna ya ajiye mukamin shugabancin kwamitin gudanarwar Bankin FMBN

Nasiru Gawuna 750x430

Nasiru Yusuf Gawuna ya ajiye mukaminsa na shugaban kwamitin gudanarwa na Bankin gidaje na tarayya FMBN.

Rahotanni sun nuna cewa Gawuna ya kammala shirye-shiryen sauya sheka tare da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, inda ake sa ran zai koma jam’iyyar ADC a ranar Talata.

A cikin wasikar murabus dinsa mai dauke da kwanan wata 27 ga watan Maris 2026, ya bayyana cewa matakin nasa ya fara aiki nan take kuma ya yi daidai da umarnin shugaban kasa domin tabbatar da bin dokokin zabe gabanin harkokin siyasa da ke tafe.

Ya nuna matukar godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu bisa damar da aka ba shi na yin aiki, yana mai cewa hakan wata dama ce ta bayar da gudummawa ga ci gaban bankin da kasa baki daya.

Ya kara da cewa matakin nasa ya biyo bayan umarnin shugaban kasa da ya bukaci duk masu rike da mukaman siyasa su sauka bisa tanadin dokar zabe.

Ya kuma tabbatar da cewa zai mika ragamar ayyukansa yadda ya dace tare da neman yardar Allah kan mataki na gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here