Gwamna Zulum ya rusa majalisar zartarwa ta Borno

WhatsApp Image 2024 10 05 at 11.23.50 750x430

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da rusa majalisar zartarwa ta jihar nan take.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Bukar Tijani, ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin samar da yanayi mai kyau ga duk wani mamba na majalisar da ke son tsayawa takara a zabukan da ke tafe.

A cewar sanarwar, Zulum ya umarci dukkan kwamishinoni da su mika ragamar ma’aikatunsu ga manyan sakatarori kafin ranar Juma’a, 3 ga watan Afrilu, 2026.

Sanarwar ta kuma nuna cewa gwamnan ya bayyana matukar godiya ga kwamishinonin da suka kammala aikinsu bisa jajircewa, kwarewa da gudummawar da suka bayar wajen ci gaban jihar da hidimar al’umma.

Majiyoyi sun nuna cewa wannan mataki na iya kasancewa yana da nasaba da bukatar bai wa wadanda ke da niyyar tsayawa takara damar shiga harkokin siyasa kafin zabukan da ke tafe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here