Rundunar sojin Najeriya ta tura dakaru 197 Gambia don bada gudunmawar tsaro

IMG 20250620 124316 768x576 1 750x430

A ranar Juma’ar da ta gabata ce rundunar sojin Najeriya, ta tura dakaru 197 zuwa tawagar kungiyar ECOWAS da ke Gambia ECOMIG.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa sojojin 197 ɗin sun samu horo ne a cibiyar Martin Luther Agwai International Leadership and Peace Keeping Center da ke Jaji Cantonment a Kaduna.

Babban Bako na Musamman, Babban Hafsan Soji Manjo Janar Uwem Bassey, ya ce an ba su tsantsar horo ne tare da shirya su don gudanar da ayyukansu.

Bassey, wanda ya samu wakilcin mataimakin babban hafsan soji na rundunar sojojin kasa Manjo Janar Ishaya Madina, ya ce, Najeriya na da daɗaɗɗen tarihi wajen bayar da gudunmawa ga kokarin wanzar da zaman lafiya a duniya, inda dakarun wanzar da zaman lafiya na Najeriya ke samun karɓuwa a duniya saboda jajircewa da kwarewarsu.

Ya ƙara da cewa, ana sa ran sojojin za su kiyaye da’a da nuna rashin son kai, da lura da mutuncin Dan-adam yayin gudanar da aikinsu a Gambia.

Bassey ya jaddada mahimmancin hana aikata lalata da duk wani cin zarafi,inda ya ƙara da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Tun da farko a nasa jawabin, kwamandan cibiyar Manjo Janar Ademola Adedoja, ya ce,  a rubu’in farko na wannan shekarar, cibiyar ta samu nasarar horas da dakarun wucin gadi na Majalisar Dinkin Duniya 3.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here