Rundunar ‘ƴan sanda a jihar Abiya ta kama wani mutum da ake zargi da harbe ɗansa bayan da ya fusata saboda ya cinye abinci.
Lamarin ya faru ne a yankin Eziama Lokpaukwu da ke ƙaramar hukumar Umunneochi a jihar Abiya.
Shaidu sun ce ɗan ya shiga gidan inda ya ɗauki abincin da aka ajiye a tukunya tare da cinyewa.
Lamarin ya fusata mahaifinsa saboda rashin neman izini kafin cinye abincin sai kuma suka ce ya shiga ɗaki tare da harbe ɗansa.
Karin labari: Benin za ta aika da jami’an tsaro sama da 1,000 zuwa Haiti
Mutanen yankin sun fusata inda suka damke mahaifin tare da ƙulle shi kafin ‘ƴan sanda su bayyana.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar Maureen Chinaka ta tabbatarwa da BBC faruwar lamarin.
Ta ce rundunar ‘ƴan sandan ta samu rahoto game da lamarin inda jami’ai suka cafke shi tare da ɗauke gawar yaron domin gudanar da bincike a kanta.
Maureen Chinaka ta ƙara da cewa an miƙa batun ga sashen da ke lura da manyan laifuka domin ci gaba da bincike.













































