Jamhuriyar Benin na shirin tura jami’an ‘yan sanda da sojoji sama da 1,000 zuwa ƙasar Haiti domin taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci a yankin Caribbean, kamar yadda gidan rediyon Faransa RFI ya rawaito.
Duk da yake ba’a bayar da sanarwar a hukumance ana ci gaba da shirye-shiryen ba.
Ministan harkokin wajen Benin Olushegun Bakary da babban hafsan sojin kasar Janar Fructueux Gbaguidi sun halarci taron ministocin harkokin wajen ƙasashen G20 da aka yi a Brazil a makon jiya domin tattaunawa da gabatar da shirye-shiryen tura jami’an tsaron.
Karin labari: Mutum 5 sun mutu bayan rushewar gini mai hawa biyu a Anambra
An kiyasta jimillar tawagar jami’an tsaron tsakanin 1,000 zuwa 1,500.
Ƙasar Benin dai tana da tarihin bayar da gudunmawar jami’an tsaro ga ayyukan tabbatar da zaman lafiya a Haiti tun daga shekarar 1994.
Sai dai kuma tawagar Haiti karkashin jagorancin Kenya ta fuskanci tsaiko saboda kalubalen shari’a, da karancin kudade, da kuma batutuwan kayan aiki.