
Gwamnan jihar Anambra Farfesa Charles Soludo, ya tabbatar da mutuwar mutum 5 da jikkatar wasu 26 sakamakon rushewar wani gini mai hawa biyu a kasuwar Odu-Igbo a birnin Onitsha.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wurin da lamarin ya faru bayan da ya je domin duba ibtila’in.
A cewar gwamnan, gwamnati za ta biya kuɗin maganin mutanen da ke samun kulawar likitoci a asibitoci.
Karin labari: An yi nasarar kwaso ‘yan ci rani 147 da suka makale a Libya
Ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a lamarin.
Gwamnan ya kuma umarci ɗan kwangilar da ke kula da ginin da ya kawar da ɓuraguzon ko ya fuskanci fushin hukuma.
Ya ce gini ba bisa ƙa’ida ba na ci gaba da zama babban ƙalubale da jihar ke fuskanta.
Ya kuma ba da umarnin cewa sai an samu amincewar gwamnati kafin tada gini a duk wata kasuwar jihar Anambra.












































