An yi nasarar kwaso ‘yan ci rani 147 da suka makale a Libya

Mazauna, Libya, 'yan ci rani, libya, makale, yan najeriya
Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar hukumar kula da ‘yan cirani ta duniya IOM sun yi nasarar dawo da wasu ‘yan ci rani 147 ‘yan Najeriya da suka makale...

Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar hukumar kula da ‘yan cirani ta duniya IOM sun yi nasarar dawo da wasu ‘yan ci rani 147 ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Libya.

Ambasada Kabiru Musa, mai kula da harkokin ofishin jakadancin Najeriya a Libya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata.

Musa ya ce ana sa ran kwashe mutanen da suka tashi daga filin jirgin saman Tripoli a ranar Talata a cikin hayar jirgi mai lamba UZ 189 za su isa filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Legas a wannan rana da yamma.

Karin labari: Babban bankin Najeriya ya ƙara yawan kuɗin ruwa

“A ci gaba da atisayen kwashe ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Libya, da gwamnatin tarayya ke ci gaba da yi, wanda hukumar IOM ke tallafawa a Libya, mun yi nasarar kwashe wasu ‘yan ci rani 147 da suka makale a Libya. Wadanda aka kora sun hada da maza 78 da mata 55 da yara 13 da jariri 1.

Sun bar kasar Libya cikin nasara kuma ana sa ran za su isa filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Legas, inda jami’an da abin ya shafa za su tarbe su” in ji shi.

Ya kara da cewa, “za mu ci gaba da kwashe ‘yan Najeriya da suka makale da suka bayyana aniyar komawa Najeriya a karkashin shirin IOM na sa kai na ‘yan gudun hijira VHR, bisa ga sabon tsarin da gwamnatin yanzu ke da shi don tabbatar da cewa dukkan ‘yan kasar sun sami ingantacciyar rayuwa.

Karin labari: Fada da ’Yar Sanda ya kai wata matashiya gidan Yari

Har ila yau, mun gamsu da atisayen komawa gida da ake yi a kai a kai, wanda ya nuna cewa da yawa daga cikin ‘yan Najeriya na son komawa gida don bayar da tasu gudunmawar ga ci gaban kasa,” inji Musa.

Musa ya nuna godiya ga hukumomin Libya, wadanda a kowane lokaci su ke goyon bayan atisayen nasara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here