Shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ziyarci ministan babban nirnin tarayya, Nyesom Wike, a ranar Talata, a gidansa da ke Abuja.
An bayyana ziyarar a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ministan, Lere Olayinka, ya fitar a shafin X.
Olayinka ya rubuta cewa “Shugaban majalisar dattawa na kasa, Godswill Akpabio, yayin ziyarar da ya kai wa Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, a gidansa a yau.”
Hakan na zuwa ne bayan da aka ayyana dokar ta baci a jihar Ribas da ta kai ga dakatar da gwamna da mataimakiyarsa da kuma majalisar dokokin jihar na tsawon watanni 6.
Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a fitar da wata sanarwa a hukumance kan abinda suka tattauna a ganawar ta su ba.