Kansiloli bakwai daga cikin 11 na karamar hukumar Ijebu- Gabas ta jihar Ogun a ranar Alhamis sun ce sun dakatar da shugaban karamar hukumar Mista Wale Adedayo na tsawon watanni uku.
Kansilolin sun sanar da dakatarwar ne ta wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban majalisar dokokin Ijebu-gabas, Hon. Akindele Fasheyi, da wasu shida.
A cikin wasikar da aka rabawa manema labarai a Abeokuta, kansilolin sun ce an dakatar da Adedayo ne sakamakon zargin almundahana da kudade.