Kotu ta tisa keyar wata matashiya zuwa gidan yari saboda kaiwa wata ’yar sanda hari a yankin A’jah da ke Jihar Legas.
Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta gurfanar da matar mai shekaru 26 ne bayan da kyamara kan titi ta kama ta tana cin zarafin wata ’yar sanda.
Karin labari: ‘Ƴan kasuwar Nijar sun yi watsi da ƙayyade farashin shinkafa
Kakakin rundunar Benjamin Hundeyin, ya bayyana hakan a ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu a shafinsa na X.
Hundeyin ya ce “Mun gurfanar da wata ’yar shekara 26 a gaban kuliya bisa mummunan hari da ta kaiwa wata ’yar sanda, bayan da kyamara ta dauko hoton cin zarafin a ranar 21 ga Fabrairun 2024.
Karin labari: Babban bankin Najeriya CBN ya fara sayar da Dala ga BDC
“Washe gari aka gurfanar da ita a gaban kotun majistare ta Etiosa, Ajah an tasa keyarta zuwa gidan yarin Kirikiri har zuwa ranar zama na gaba, 27 ga watan Maris, 2024.