Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi nasarar lashe tikitin takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a karkashin jam’iyyar NNPP.
A zaɓen da aka gudanar a ƙaramar hukumar Gezawa ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da ke ƙarƙashin majalisar dattawa, Malam Ibrahim Shekarau ya samu ƙuri’u 516.
Shekarau, wanda shi ne Sanata mai wakiltar shiyyar a majalisar dokokin Najeriya, a jawabinsa, ya gode wa Allah maɗaukakin sarki da ya sanya aka samu nasarar kammala zaɓen cikin nasara.
Solacebase ta ruwaito cewa a kwanakin baya ne Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga jam’iyyar APC zuwa NNPP.












































