Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da wasu dandalin sa ido da bibiyar ayyuka don tabbatar da gaskiya

Abba Kabir Yusuf Kano Kano 715x430

Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da dandali biyu na zamani da suka haɗa da tsarin sa ido kan ayyukan gwamnati na jihar Kano da kuma manhajar Fix Kano a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa gaskiya, ɗaukar alhaki da haɗa jama’a cikin tafiyar mulki.

Ci gaban na zuwa ne a cikin wata sanarwa da mataimakin mai ba gwamna shawara na musamman kan shirin buɗaɗɗen shugabanci, Musaddiq Kabir Adam, ya fitar, inda ya nuna cewa an ƙaddamar da dandalan ne domin inganta tsarin mulki da bude kofa ga kowa a jihar.

Sanarwar ta bayyana cewa an ƙirƙiri dandalan ne a ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, domin ƙarfafa bayyana shugabanci da inganta alaƙar gwamnati da al’umma ta hanyar gudanar da harkokin jama’a cikin gaskiya da haɗin kai.

Karanta: Gwamnatin tarayya ta fara gina titin Jakara-Wuju-Wuju a kan Naira biliyan 47 a Kano

Ta ƙara da cewa tsarin sa ido kan ayyukan gwamnatin jihar Kano na bai wa mazauna jihar damar bibiyar ayyukan gwamnati kai tsaye, tare da samun bayanai kan kasafin kuɗi, jadawalin aiwatarwa da rahotannin cigaba, domin tabbatar da amfani da kuɗin jama’a yadda ya kamata da kuma kammala ayyuka a kan lokaci.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa manhajar Fix Kano tana bai wa ‘yan ƙasa damar kai rahoton matsalolin da suka shafi ayyukan jama’a da ababen more rayuwa, inda hakan ke buɗe hanya kai tsaye tsakanin jama’a da gwamnati tare da ba masu amfani damar bibiyar yadda ake warware matsalolin da suka kai rahoto a kai.

Sanarwar ta kuma nuna cewa waɗannan tsare-tsaren sun yi daidai da sabon shirin aikin bayyana shugabanci na jihar Kano na shekarun 2024 zuwa 2026, wanda ya fi mayar da hankali kan inganta ayyukan jama’a, yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma ƙara sa hannun ‘yan ƙasa a harkokin mulki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here