Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Dalhatu, Are da Oke a matsayin jakadu

Senate 1 750x430

Majalisar Dattawa ta ƙasa ta tabbatar da naɗin Aminu Dalhatu, Kayode Are da Ayodele Oke a matsayin jakadu marasa aiki bayan kammala tantance su a zauren majalisar.

Aminu Dalhatu tsohon wakilin ƙasa ne a harkokin diflomasiyya, yayin da Kayode Are kuma tsohon babban darakta ne na Hukumar Tsaron Cikin Gida, shi kuma Ayodele Oke ya taɓa rike muƙamin babban darakta na Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa.

Majalisar ta amince da naɗin nasu ne bayan shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ƙasashen waje, Sanata Sani Bello, ya gabatar da rahoton tantancewa mai gamsarwa ga ‘yan majalisar.

Rahoton ya nuna cewa sunayen mutanen ukun na cikin jerin farko daga cikin jerin sunayen da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya turawa Majalisar dattawan ƙasa kusan makonni biyu da suka gabata domin amincewa.

A cewar bayanan da aka gabatar wa majalisar, Aminu Dalhatu ɗan jihar Jigawa ne, yayin da Kayode Are da Ayodele Oke dukkansu ‘yan jihar Ogun ne.

A wani ci gaba da ya shafi zaman majalisar, Majalisar dattawan ƙasa ta kuma tabbatar da naɗin Dakta Chukwuemeka J. Chukwu a matsayin kwamishinan zaɓe mai zaman kan sa a jihar Abia a Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, bayan rahoton tantancewa da kwamitin majalisar kan harkokin zaɓe, ƙarƙashin jagorancin Sanata Simon Lalong, ya gabatar.

Haka kuma, Majalisar ta tabbatar da naɗin Dakta Animashaun Olayinka da Uwargida Aisha Kanti Bello a matsayin mambobin kwamitin gudanarwa na Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa, bayan rahoton tantancewa da kwamitin majalisar kan wutar lantarki, ƙarƙashin jagorancin Sanata Eyinnaya Abaribe, ya gabatar, wanda Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gabatar da sunayensu domin naɗin makonni kaɗan da suka gabata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here