CBN ya ƙaryata jita-jitar korar Emefiele

CBN
CBN

Babban bankin Najeriya CBN ya ce, rahotonnin da wasu kafafen yaɗa labarai Internet ke yaɗawa kan korar gwamnan banking Mista Godwin Emefiele, ba gaskiya ba ne.

Shugaban sashen sadarwa na CBN, Osita Nwanisiobi ne ya bayyana hakan yau Laraba a Abuja lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN.

A halin yanzu Emefiele yana kasar waje inda yake aiki a hukumance.

NAN ta ruwaito cewa Emefiele ya kasance a idon jama’a tun bayan da ya bayyana sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a zaɓen 2023 mai da ke tafe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here