2023: Mohammed Abacha ya zama dan takarar gwamna na PDP a kano

moh
moh

Alhaji Mohammad Abacha, dan tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, Janar Sani Abacha ya zama dan takarar gwamnan Kano a jam’iyar PDP na za6en 2023.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, Muhammad Abacha ya samu kuri’u 736, wanda ya ba shi damar kayar da Jafar Sani Bello wanda shi ne ya zo na biyu, da kuri’a 710 a za6en fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar ranar Laraba a jihar kano.

Shugaban kwamatin za6en, Alhaji Muhammad Jamu, ya ce za6en ya gudana bisa doka da ka’idoji, da kuma sa idon hukumar za6e ta kasa INEC, jami’an yan sanda da sauran jami’ai na jahar Kano.

Sai dai kuma wani tsagi na jam’iyar, shi ma ya gudanr da za6e na daban a cibiyar hosar da matasa sana’o’i ta Abacha youth Center, bayan za6en da ya gudan a shalkwatar jam’iyyar ta PDP na jaha, wanda ya ayyana Muhammad Abacha a matsayin dan takara gwamna na jam’iyar.

Yan takarar da suka shiga za6en da aka gudanar a cibiyar horas da sana’o’in sun hada da Mu’az Magaji, Ibrahim Al-Amin, Sadiq Wali, Mutapha Getso, Yusuf Dambatta da kuma Yanusa Dangwani.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here