DA DUMI-DUMI: Kotu ta kori ‘yan majalisar jihar Cross River 20 saboda sauya jam’iyya

BREAKING 2
BREAKING 2

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta kori ‘yan majalisar dokokin jihar Cross River su 20 da suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Kotun, a ranar Litinin, a wani hukunci da mai shari’a Taiwo Taiwo, ya yanke, ta ce ‘yan majalisar sun yi watsi da jam’iyyar siyasar da ta kai su ga karagar mulki, ya kamata su bar kujerunsu.

Hukuncin ya biyo bayan karar mai lamba FHC/ABJ/CS/975/2021, wadda PDP ta shigar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here