Gwamnatin plateau ta sanya dokar hana fita na awanni 48 a karamar hukuma

Plateau map

Gwamnatin jihar Plateau ta sanya dokar hana fita na tsawon awanni 48 a karamar hukumar Jos ta Arewa da ke jihar.

Kwamishinar yada labarai da sadarwa ta jihar, Joyce Ramnap, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin a Jos.

Ramnap ta ce an dauki wannan mataki ne bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a daren Lahadi a unguwar Angwan Rukuba da ke yankin.

Rahotanni sun nuna cewa harin da ya faru da misalin karfe 8 na dare ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 12, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Ta ce gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar jami’an tsaro sun sanya dokar hana fita a fadin karamar hukumar Jos ta Arewa.

Ta kara da cewa dokar za ta fara aiki daga tsakar dare na ranar Lahadi, 29 ga Maris, zuwa ranar Laraba, 1 ga Afrilu.

Kwamishinar ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa fararen hula ba tare da wani dalili ba, tare da kira ga mazauna yankin da su kasance masu bin doka da oda.

Ta kuma tabbatar da cewa gwamnati tare da jami’an tsaro sun dauki matakan hana sake aukuwar irin wannan hari tare da kamo wadanda suka aikata laifin.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here