Yadda Kwankwaso ya yaudareni-Shekarau

IMG 20220822 125222 238 scaled 1
IMG 20220822 125222 238 scaled 1

Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya musanta zancen dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, na cewa abinda ya sa ba’a biya musu bukatun su ba shine shiga jam’iyyar da suka yi a makare.

Jaridar Solacebase ta ruwaitu cewa a wata hira da akai da Rabiu Musa Kwankwaso, akan rigimar da ke faruwa a tsakanin mutanan Shekarau da mutanan sa, Kwankwaso ya ce lokacin da su Shekarau suka bada jerin guraben da suke bukata a basu, INEC ta rufe karbar sunayen ‘yan takarkaru.

Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da jam’iyyun adawa suke zawarcin Malam Ibrahim Shekarau, da ya kuma jam’iyyun su, kamar jam’iyyar adawa ta PDP wacce rahotoni ke nuni da cewa Shekarau ya gama shiryawa tsaf da Wazirin Adamawa, na ya koma jam’iyyar.

Ya yin da yake yiwa magoya bayan sa da kuma kwamitin Shura bayani a Kano ranar Litinin, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana musu yacce aka yaudareshi bayan komawar sa jam’iyyar NNPP.

Shekarau ya ce sun mikawa Sanata Rabiu Kwankwaso, jerin bukatun su sama da wata uku kafin INEC ta rufe karbar sunayen ‘yan takarkaru.

Ya ce kwamitin da Kwankwaso ya kafa a ranar 16 ga watan Mayu na shekarar 2022, wanda zai aiki cikin kwanaki uku, ya gaza magance matsalar sama da watanni uku da suka wuce.

Ya kuma kara da cewa koda ya fita daga APC, ba wai shi kadai ya yanke hukunci ba, sai da ya tun tubi magoya bayan sa da kuma kwamitin Shura kafin ya fita.

Ya ce wannan karan ma magoya bayan sa da kuma kwamitin Shura sune zasu kara yanke wukunci makomar sa, nan da kwanaki biyu masu zuwa.

Shekarau ya kuma musanta zargin da ake masa na cewa zai bar jam’iyyar ta NNPP ne saboda ya sami kudi a jam’iyyar adawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here