Shugabar Mata ta jami’iyyar APC, Kemi Nelson ta rasu tana da Shekaru 66

Late Kemi Nelson
Late Kemi Nelson

Uwargida Kemi Nelson, tsohuwar mataimakiyar shugabar mata ta jam’iyyar APC ta kasa ta rasu, kamar yadda wata majiya mai tushe daga jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta bayyana a ranar Lahadi.

Kafin rasuwar Kemi Nelson, ta kasance tsohuwar babbar darakta ce ta asusun Inshora na Nigerian Social Investment Trust Fund.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, ya ruwaito cewa Nelson, wadda tsohuwar kwamishina ce a jihar Legas ta rasu ne bayan doguwar jinya tana da shekaru 66.

Wata majiya mai tushe a jam’iyyar APC ta shaida wa manema labarai cewa gaskiya ne jigon jam’iyyar ta rasu bayan ta sha fama da rashin lafiya.

Sai dai majiyar ta ki amsa wasu tambayoyi kan rasuwar tsohuwar shugabar Matan ta APC.

Nelson ita ce mace daya tilo a Majalisar Shawarar Mulki ta jam’iyyar APC reshen jihar Legas.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada ta matsayin babbar daraktar hukumar NSITF a shekarar 2019, inda ta rike har zuwa watan Mayun shekarar da ta gabata ta 2021.

An haife ta a ranar 9 ga watan Fabrairu, na shekarar 1956, kuma ta yi makaranta a Ijebu da Legas da Ibadan kuma ta rasu ta bar ‘ya ’ya uku.

Kafin rasuwarta, Nelson ta kasance Yeye Oge din jihar Legas kuma daya daga cikin ta hannun damar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here