Gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da Sarkin Sabuwar Masarautar Yandoto

Ado Alerus turbaning ceremony took place on July 16 2022. 1
Ado Alerus turbaning ceremony took place on July 16 2022. 1

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya amince da dakatar da Sarkin sabuwar Masarautar Birnin Yandoto, Alhaji Aliyu Marafa, bisa bawa wani Dan ta’adda da ake nema ruwa a jallo, Adamu Aliero-Yankuzo, wanda aka fi sani da Ado Alero, mukami a masarautar.

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa tana neman Alero ne tun a shekarar 2020 kan kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane a jihohin Zamfara da Katsina.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a ranar Asabar din da ta gabata ne Sarkin Yandoto Daji, Aliyu Garba Marafa ya nada Ado Alero a matsayin Sarkin Fulanin Masarautar Yandoto.

An gudanar da bikin nadin Aleron, bayan sa’o’i kadan kuma aka dakatar da ayyukan masarautar har illa masha Allah.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu shugabannin kungiyar ‘yan bindiga sun shaida bikin a kan babura da dama don yin murna ga Aliero.

Dakatar da Sarkin na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Alhaji Kabiru Balarabe, ranar Lahadi.

Kazalika gwamnatin jihar ta kuma kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan lamarin.

Mambobin kwamitin sun hadar da Hon. Yahaya Chado Gora a matsayin shugaba da Hon. Yahaya Mohd Kanoma a matsayin mamba, sai Hon. Muhd Umar B/Magaji shi ma mamba.

Sauran sune Hon. Lawal Abubakar Zannah da Isa Muhd ​​Moriki a matsayin mambobi da kuma Barrista Musa Garba, a matsayin Sakatare.

A cewar sanarwar, Sakataren Gwamnatin Jihar ya ce, a halin da ake ciki, Alhaji Mahe Garba Marafa, wanda shi ne Hakimin ‘Yandoto, an nada shi don kula da harkokin masarautar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here