PSC ta tantance masu neman aikin ‘Yan Sanda da za suyi CBT

'yan sanda, PSC, CBT, nema, tantance
Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda PSC ta tantance mutane 171,956 da za su yi jarrabawar Kwamfuta ta CBT a ci gaba da daukar ma’aikata ga masu neman aiki a...

Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda PSC ta tantance mutane 171,956 da za su yi jarrabawar Kwamfuta ta CBT a ci gaba da daukar ma’aikata ga masu neman aiki a matsayin ‘yan sandan Najeriya.

Sanarwar da ta fito a ranar Alhamis a Abuja ta hannun Mista Ikechukwu Ani shugaban yada labarai da hulda da jama’a na PSC ya ce za’a fara CBT a ranar 5 ga watan Maris na shekarar 2024.

Karanta wannan: Farashin kayan abinci ya tashi zuwa kaso 29.90 a Najeriya – NBS

Ya ce wadanda aka bayyana za suyi CBT su ne wadanda suka yi nasara a sakamakon kammala aikin tantancewar da aka gudanar a fadin kasar.

A cewarsa, ‘yan takara kimanin mutum 171,956 da za’a yi jarrabawar cancantar su ne masu neman mukamai na gama-gari.

Ya cigaba da cewa, “Bayan wani taro da hukumar daukar ma’aikata ta ‘yan sanda ta yi, ta amince da cewa hukumar ta hadin gwiwa ce ta gudanar da hukumar ta CBT, saboda kasancewar ta da dadewa a irin wannan jarrabawa” inji shi.

Karanta wannan: Tinubu ya gana da gwamnoni kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi da tsaro

Ya kara da cewa ‘yan takarar da suka yi nasara daga CBT za’a bukaci su bayyana a duba lafiyarsu kafin a ci gaba da samun horo.

Ani ya yi alƙawari shugaban PSC Dakta Solomon Arase ya yi kan kammala atisayen a kan lokaci don gaggauta shigar da waɗanda suka yi nasara a cikin tsarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here